10 Mayu 2020 - 05:17
​Gwamnatin Mali Ta Janye Dokar Hana Kai Komo A Kasar

A kasar Mali mahukunta sun sanar da janye dokar takaita zirga-zirga cikin dare da aka sanya fiye da wata daya da ya gabata, domin dakile yaduwar cutar corona a kasar.

(ABNA24.com) A kasar Mali mahukunta sun sanar da janye dokar takaita zirga-zirga cikin dare da aka sanya fiye da wata daya da ya gabata, domin dakile yaduwar cutar corona a kasar.

Bayan sanar da hakan, mahukuntan na Mali sun jaddada wajabcin sanya takunkumin fuska a kan kowa a lokacin shiga cikin jama’a da kuma sauran mu’amaloli na yau da kullum.

Haka nan kuma mahukuntan sun yi gargadin cewa cutar ta shiga kusan ko ina a yankunan kasar, a kan akwai bukatar a kara yin gwaji a kan mutane domin kara tantance wadanda suke dauke da cutar.

Bisa sanarwar hukumomin kiwon lafiya na kasar ya zuwa yau, akwai kusan 700 da aka tabbatar sun kamu da cutar a kasar, yayin da wasu 35 daga cikinsu kuma suka rasa rayukansu.

Kasar Mali na daga cikin kasashen Afrika da ake fargabar cewa idan cutar ta barke za ta yi babbar illa ga jama’a, saboda matsaloli na karancin kayayyakin aiki a kasar.



/129